20 Afirilu 2020 - 06:32
​ Iran : Zarif Zai Gana Da Shugaban Siriya A Wannan Litini

A wani lokaci a gobe Litini ce ake sa ran ministan harkokin wajen

(ABNA24.com) kasar Iran, Mohammad Javad Zarif, zai kai wata ziyarar aiki a kasar Siriya.

Wata sanarwa da ma’ikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta ce yayin ziyarar Mista Zarif, zai gana da shugaban kasar ta Siriya, Bashar Al-Assad.

Sannan zai kuma gana da takwaransa na Siriya Walid al-Mouallem.

Bangarorin zasu tattauna kan batutuwan da suka shafi alakar dake tsakanin kasashen da halin da ake ciki a yankin, da kuma batun yaki da ta’addanci a kasar ta Siriya, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Abbas Moussavi, ya sanar.

/129